Romans 7

1‘Yan’uwa, ko baku sani ba (domin ina magana da wadanda suka san shari’a), cewar shari’a na mulkin mutum muddin ransa?

2Domin ta wurin shari’a matar aure a daure take muddin mijinta nada rai, amma idan mijinta ya mutu, ta kubuta daga shari’ar aure. 3To don haka idan, mijinta na da rai, sai ta tafi ta zauna da wani mutumin, za’a kirata mazinaciya. Amma idan mijin ya mutu, ‘’yantarciya ce daga shari’a, domin kada ta kasance mazinaciya idan ta auri wani mutum.

4Domin wannan, ‘yan’uwana, ku ma an sa kun mutu ga shari’a ta wurin jikin Almasihu, saboda a hada ku aure da wani, wato, ga wanda aka tashe shi daga matattu, domin mu haifawa Allah ‘ya’ya. 5Domin sa’adda muke cikin jiki, ana motsa dabi’armu ta zunubi dake cikin jikunan mu ta wurin shari’a domin mu haifi ‘ya’ya zuwa mutuwa.

6Amma yanzu an kubutar damu daga shari’a, mun mutu daga abin da ya daure mu, domin mu yi bauta cikin sabuntuwar Ruhu, ba cikin tsohon rubutun shari’a ba.

7To me zamu ce kenan? ita shari’ar kanta zunubi ce? ba zai taba faruwa ba. Duk da haka. Idan ba ta wurin shari’a ba, ba zan taba sanin zunubi ba, in ba ta wurin shari’a ba. Ba zan taba kyashin abin wani ba, har sai da shari’a tace, “Kada kayi kyashi.” 8Amma zunubi, sai ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya jawo dukkan sha’awa dake cikina. Domin in da babu shari’a, zunubi matacce ne.

9Ada na rayu sau daya ba tare da shari’a ba, amma da dokar ta zo, sai zunubi ya farfado, ni kuma na mutu. 10Dokar wadda ta kamata ta kawo rai, sai na same ta matacciya.

11Domin zunubin, ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya rude ni, kuma ta wurin dokar ya kashe ni. 12Domin haka, shari’ar na da tsarki, dokar na da tsarki, adalci da kuma kyau.

13To abu mai kyau ya zamar mani mutuwa kenan? ba zai taba zama haka ba. Amma zunubi, domin ya nuna shi zunubi ne ta wurin abin da ke mai kyau, sai ya kawo mutuwa a cikina. Wannan ya kasance haka ne domin ta wurin dokar, zunubi ya zama cikakken zunubi. 14Domin mun san shari’a mai Ruhaniya ce, amma ni ina cikin jiki. An sai da ni karkashin bautar zunubi.

15Domin ni ma ban fahimci abin da nake aikatawa ba. Domin abin da nake so in aikata, ba shi nake aikatawa ba, kuma abin da bana so, shi nake aikatawa. 16Amma idan na aikata abin da bana so, na amince da shari’a kenan, cewar shari’a nada kyau.

17Amma yanzu ba ni ke aikata abin ba, amma zunubi da ke zaune a cikina. 18Domin na san a cikina, wato cikin jikina, babu wani abu mai kyau. Domin marmarin aikata abu mai kyau na tare da ni, amma ba ni iya aikatawa.

19Domin abu mai kyau da na ke so in aikata bana iyawa, amma muguntar da ba na so ita na ke aikatawa. 20To idan na yi abin da ba ni so in aikata, wato kenan ba ni bane ke aikatawa, amma zunubin da ke zaune a cikina. 21Don haka, sai na iske, akwai ka’ida a cikina dake son aikata abu mai kyau, amma kuma ainihin mugunta na tare dani.

22Domin a cikina ina murna da shari’ar Allah. 23Amma ina ganin wasu ka’idoji daban a gabobin jikina, su na yaki da wannan sabuwar ka’idar da ke cikin tunanina, suna kuma sanya ni bauta ta wurin ka’idar zunubi wadda ke cikin gabobin jikina.

24Ni wahalallen mutum ne! wa zai kubutar dani daga wannan jiki na mutuwa? Amma godiya ga Allah ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Domin haka ni kaina a wannan hannu bisa ga tunani na ina bautawa shari’ar Allah. Duk da haka, ta wani gefen ina bautawa ka’idar zunubi da ke tare da jikina.

25

Copyright information for HauULB